PDP na son batawa EFCC suna — APC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jam'iyyun APC da PDP sune manya da ke adawa da juna a Najeriya.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce tana sane da irin yadda babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke matukar adawa da yakin da shugaba Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar APC ta ce tana kuma sane da shirin da PDP ke yi na wargaza tare da neman batawa hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa suna.

A baya-bayan nan jam'iyyar PDP ta fitar da sanarwa daban-daban inda take zargin APC da yi wa mambobinta bi-ta-da-kulli da bata musu suna wajen zargin cin hanci da rashawa.

Halima Umar Saleh, ta ga dukkan sanarwar ga kuma rahoton da ta hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti