Merkel:Za mu hukunta yan cirani masu laifi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da wasu shawarwari da za su saukaka tasa keyar masu neman mafaka a cikin kasar da suka aikata munanan laifuka.

Ta na maida martani ne ga bukatar Jam'iyyarta ta CDU na daukar kwakkwarar mataki bayan lamarin da ya faru na sace sace da cin zarafin mata a Cologne a jajiberin sabuwar shekara wanda aka danganta da wasu masu neman mafaka a kasar.

Da ta ke jawabi bayan wani taro na shugabannin jam'iyyarta Mrs Merkel ta ce dole ne a yi hukunci a kan mutanen da karya doka.

Sai dai kuma shugabar gwamnatin ta jaddada bukatar inganta sajewar 'yan cirani ciki al'amuran rayuwar yan kasa ta yau da kullum