Za a tasa-keyar Guzman Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan shi ne karo na uku da ake kama El-Chapo, kuma ana shirin tasa keyarsa zuwa Amurka.

Ofishin babban mai shigar da kara na kasar Mexico ya ce za a fara shirin fitar da tantirin madungun miyagun kwayoyin nan na garin Sinaloa, Joaquim Guzman, zuwa kasar Amurka.

An sake kama Guzman ne a ranar Jumma'a, bayan da ya tsere daga wani babban gidan kaso a karo na biyu watanni shida da suka gabata.

A baya dai kasar ba ta amince da bukatar Amurkan na a tasa-keyar Guzman din kasar ta ba, amma yanzu hukumomin kasar Mexicon sun sauya shawara.

Ga dukkanin alamu Mexicon sun gano cewar madugun miyagun kwayoyin na barazana ga tsaron kasar, saboda damar da ya ke samu na saye jami'an kasar ta hanyar karbar hanci da rashawa.

Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da ranar da za a saurari karar a kotu ba, amma masu shigar da karar gwamnatin kasar sun ce za a bai wa lauyoyin Guzman din kwanaki uku domin su shirya.