An yi wa shafin Tuwitar Jeremy Corbyn kutse

Image caption Jeremy Corbyn

Masu kula da shafin Tuwitar shugaban jam'iyyar adawa ta Labour a Birtaniya, Jeremy Corbyn sun shawo kan shafin ne bayan wanda ya yi kutsen ya samu nasarar tura wasu sakonni hudu.

Wanda ya yi kutsen ya yi amfani da wasu munanan kalamai wajen wallafa sakonnin.

An aibanta Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron a cikin daya daga cikin sakonnin, inda aka ce David Cameron "holoko" ne.

Wasu 'yan sa'o'i kadan aka yi da kutsen, amma duk da haka an tura sakonnin zuwa ga mabiyansa 384,000.

Sai dai suna kwato shafin tuwitar ba su tsaya wata-wata ba suka share dukkan sakonni hudun.

Galibi sakonnin da jagoran jam'iyyar Labour kan tura ba sa wuce lamuran da suka shafi siyasa, amma wanda ya yi kutse sai ya fara tuwa wani sako mai cike da motsin-rai har sau uku, alamar da ka iya sa mabiyan Corbyn din su fara zargin cewa akwai matsala.