An samu sinadaran riga-kafin dundumi

Image caption Wata mai fama da dundumi a Najeriya

Masu bincike sun wasu sinadarai uku da za a iya sarrafa su wajen yin allurar riga-kafin makanta, wadda kudan bakin kogi ke haddasawa.

Wannan cuta ta makanta dai na kama kimanin mutum miliyon 17 a kowace shekara, kuma sama da kashi 90 bisa dari na masu kamuwa na fitowa ne daga yammaci da kuma Afirka ta tsakiya.

Ana dai sa ran jarraba akalla daya daga cikin alluran riga-kafin a shekara ta 2020, yayin da za a sake auna tasirinsa a shekara ta 2025.