Za a yi taron gaggawa kan Iran

Sarki Salman na Saudiyya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mabiya darikar Shia a duk fadin duniya sun nuna rashin jin dadi da kisan Sheikh Nirm

Kasar Saudiyya ta kira taron gaggawa na Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da za a yi a birnin Alkhahira na kasar Masar.

Saudiyya na son mai da martani ne akan harin da aka kaiwa ofishin Jakadancin ta da ke kasar Iran, wanda masu zanga-zanga suka kai dan nuna fushinsu akan kisan da Saudiyyar ta yi wa fitaccen malamin Shi'a Sheikh Nimr al-Nimr.

Masu aiko da rahotanni sun ce ta yi wu a ba a za cimma matsaya ba kan tattaunawar idan aka yi la'akkari da kasashen Iraqi da Labanon na samun tallafi daga kasar Iran.

Ya yin da a bangare guda kuma ake ganin wasu daga cikin kawayen Saudiyya ba su nuna cikakken goyon baya ba ga matakin da saudiyyar ta dauka.