An nemi Trump ya nemi afuwar musulma

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar dake kyautata dangantaka da Musulmai a Amurka, ta bukaci Donald Trump, dake neman jam'iyyar Republican ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar, da ya bayar da hakuri bisa fitar da wata mata Musulma daga wurin gangamin yakin neman zaben sa.

Matar mai suna Rose Hamid, ta taba yin bore na nuna adawa da kiran da Mista Trump ya yi na a hana musulmai shiga Amurka.

A wajen gangamin neman zaben nasa, bayan sauran magoya bayansa sun zauna, Rose Hamid ta ci gaba da tsayuwa, tana sanye da wata riga da aka rubuta Salam a jikinta.

Ta sha tsawa daga sauran magoya bayan Mista Trump din, a yayin da wani jami'in tsaro ke fitar da ita daga wajen taron.

Kungiyar dake kyautata dangantaka da Musulmai a Amurkan, ta ce lamarin, wani sakone mai sosa rai ga Musulmai a kasar.