An zargi 'yan Houthi da tsare mutane

'Yan tawayen Houthi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekara guda kenan da 'yan tawayen Houthi suka karbe iko da birnin Sanaa

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan tawaye na kabilar Houthi a Yemen da laifin tsare masu adawa da su a birnin Sanaa.

Human Rights Watch ta ce ta na da cikakkun bayanan da ke nuna 'yan Houthi na tsare da Mutane 35, duk da an saki wasu daga cikinsu.

Watch ta kara da cewa akwai kuma wata kungiya da ke ikirarin ta na aiki ne a madadin fiye da mutane 800 da ake tsare da su, da kuma wadanda suka bata babu labarinsu.

Fiye da shekara guda kenan da 'yan tawayen Houthi suka karbe iko da babban birnin Yemen Sanaa, duk da irin kokarin da dakarun gwamnatin kasar da dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta suka yi na fatattakarsu daga birnin.