An hallaka mutane 17 a Iraki

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Ana zargin 'yan kungiyar IS da kai harin

Majiyoyin tsaro a Bagadaza, babban birnin Iraki sun ce an kashe mutane 17 a wani hari da aka kai wani rukunin shaguna.

Wata mota ce ta fara tarwaste a wajen rukunin shagunan.

Sannan sai wasu maza suka bude wuta a ciki kuma suka tsare wasu mutanen a ciki.

Dakarun tsaron sun killace wajen sannan suka kutsa cikin ginin.

Biyu daga cikin maharan sun ta da jigidar bama-baman da ke jikinsu, inda da yawan mutanen da suka tsare suka mutu.

Sai dai an kashe 'yan bindigar biyu yayin da aka kama wasu hudu.

Mahukunta sun ce an shawo kan lamarin.