Boko Haram: Mutane sun kubuta a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau da sauran mukarrabansa sun yi layar zana

Rahotanni daga Kamaru na cewa wasu mutane shida a karshen mako sun kubuta daga hannun 'yan Boko Haram bayan an yi garkuwa da su na tsawon lokaci.

Bayanai sun ce an rike mutanen ne na tsawon watanni shidda, a wani sansani kusa da garin Gamborou da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.

Mutanen sun tsere ne bayan da sojoji suka kai wa 'yan Boko Haram hari a sansanin, abin da ya ba su damar samun tsira.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 18,000 a yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.

A yanzu haka dai kasashen tafkin Chadi sun kafa rundunar soji domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.