CBN ya daina sayar wa 'yan canji dalar Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnan CBN, Emefiele ya ce suna kokarin kare naira ne

Babban bankin Najeriya, CBN ya ce zai daina sayar da dalar Amurka ga shagunan 'yan canji domin kare darajar kudin kasar daga karyewa.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele wanda ya sanar da hakan, ya ce matakin zai hana asusun kudin ajiyar kasashen waje na kasar daga ramewa.

"Daga yanzu 'yan canji, su nemi kudin canji daga wasu hanyoyin na daban," in ji Emefiele.

CBN din ya kuma ce daga yanzu mutane za su iya ajiye kudaden kasar waje a bankunan kasar.

Faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya, ta shafi kudaden kasashen da gwamnatin Najeriya ke samu.

Bayanai sun nuna cewa kashi 95 cikin 100 na 'yan canji sun dogara ne a kan babban bankin domin samun kudaden kasar waje.

A yanzu haka dai ana sayar da kowacce dalar Amurka a kan naira 282, tun bayan da babban bankin ya sanar da daina sayarwa 'yan canji kudi.