Fitaccen mawaki, David Bowie, ya mutu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wakokin da Bowie ya yi a shekarun 1960 da 1970 ne suka fito da shi a idanun duniya.

An bayar da sanarwar mutuwar fitaccen mawaki dan Biritaniya, David Bowie.

Bowie, mai shekara 69 a duniya, ya dade yana fama da cutar daji.

Wakilansa sun ce ya mutu ne a gaban iyalansa.

Wakokin da ya yi a shekarun 1960 da 1970 irinsu su Space Oddity da Starman sun sa Bowie ya yi suna a kasashen duniya.

Baya ga wakoki, Bowie ya zama jarumin fina-finai da kuma tallan kayan-kawa.