'El Chapo': Wanene dilan miyagun kwayoyi Guzman ?

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kama Shahararren mai fataucin miyagun kwayoyin nan dan kasar Mexico, Joaquin "El Chapo" bayan ya tsere daga gidan kaso wanda hakan ya kunyata hukumomin kasar Mexico kuma ya shafi dangantakarta da Amurka.

Wannan ne karo na farko da ya ke tserewa daga gidan yari da hannun 'yan sanda.

Ga labarin dan manomi wanda ya zama attajiri sakamakon dilancin miyagun kwayoyi.

Wane ne shi?

An haife shi a shekarar 1957, kuma iyayensa manoma ne, Guzman dai ya yi sabo da fataucin miyagun kwayoyi a lokacin da ya ke aiki a wata gonar wiwi.

A matsayinsa na yaron uban gidansa, Miguel Angel Felix Gallardo, aikin Guzman a lokacin ya kunshi hulda da masu safarar miyagun kwayoyin Colombia.

Nan da nan ya yi fice, inda ya samar da kungiyar samar da kwayoyinsa, wanda ya kira Sinaloa, a shekarar 1980, wanda a lokacin shi ne ke daukan nauyin kashi daya cikin hudu na kwayoyin da ake shiga da su Amurka ta Mexico.

Jami'an tsaron Mexico, sun kama El chapo sannan aka yanke masa hukuncin daurin gidan yari na shekara 20 bayan ya kubuta daga hannun wata kungiyar dillalan miyagun kwayoyi da ke adawa da shi.

Jaridar New Yorker ta ambato ofishin Babban mai shari'a na kasar Mexico yana bayyana El- Chapo a matsayin "Mutum mai matukar son kansa da gadara, da wayo, sannan da jajircewa wajen yin duk abin da yake so".

Ya aka yi ya tsere daga gidan yari sau biyu?

Guzman ya yi tserewarsa daga gidan kason Puente Grande a karo na farko a shekarar 2001,inda rahotanni suka nuna cewar ya biya kudi ne aka saka shi a kwandon wanki.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ya yi amfani da shekaru 13 da yayi yana buye bunkasar harkokinsa kafin a kama shi a jihar Sinaloa.

Amma kuma a watan Yulin shekarar 2015, bayan ya shafe shekaru biyu a gidan kason Altiplano da ke tsakiyar kasar Mexico, sai ya kuma tserewa, a wannan karon ta cikin rami mai tsawon kilomita daya da rabi.

Mene ne Kimarsa?

Duk da cewar kasar Mexico ta yi kaurin suna wajen yawan masu fataucin miyagun kwayoyi, kowa yasan Guzman da rikici, da takaddamar da ake yi tsakaninsa da wasu kungiyoyin fataucin miyagun kwayoyi wanda hakan ya yi sandiyar mutuwar dubban mutane a yakin da ake yi a kan miyagun kwayoyi a Mexico.

Sai dai a yankinsu, Guzman gwarzo ne, mutumin da kowa ya ke yabawa.

Ya kan shiga gidan cin abinci tare da masu gadinsa, sai ya umurci masu cin abinci a gidan cin abinci su hakura da wayoyinsu, sai ya biya kudin abinci kowa a lokacin da zai bar gidan cin abincin.

Mujallar Forbes ta ce dukiyarsa ta kai dala biliyan daya.

A wata hira da mujallar Rolling stone ta yi da shi, a ranar tara ga watan Janairun shekarar 2016, Ya ce " na fi kowa kawo kwayoyi kamar hodar-ibilis da wiwi a duniya".

Guzman ya kare matsayinsa na zama madugun sayar da kwayoyi, ya na mai cewa babu ta yadda mutum zai rayu a kasa irin ta Mexico idan bai yi hakan ba, saboda halin tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ta ke ciki.

Me yasa ya zame wa hukumomin Mexico Alakakai?

Tserewar daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo na duniya daga gidan yarin da ake zato shi ne ya fi tsaro, abin kunya ne ga hukumomin Mexico.

Ya tsere ne bayan hukumomin kasar sun yi alkawalin ba za su sake barinsa ya gudu ba .

Hakkin mallakar hoto Reuters

An yi ta zargin cewa ya samu taimako daga gidan yarin, lamarin da ya sa aka kama wasu jami'an gidan yarin.

Me ya sa Amurka ta ke nemansa?

Tun a shekarar 2014, Amurka ta nemi a kai shi Amurkar domin a kama shi da laifin fataucin miyagun kwayoyi masu yawa zuwa kasar kafin yayi tserewarsa ta karshe daga gidan kaso.

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce, idan aka mika mata shi, zai iya fuskantar tuhume-tuhume na safarar miyagun kwayoyi da cuwa-cuwa da kuma aikata kisan kai.

A halin yanzu, mai yuwa hukumomi sun bayar da tabbacin cewar idan har ana so kar Guzman ya sake tserewa, to sai dai a aike da shi Amurkar.