Kotu ta ki bayar da belin Hama Amadou

Hakkin mallakar hoto

Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta ki bayar da belin Shugaban 'yan hamayya a zaben kasar da za a yi a watan gobe, Hama Amadou.

An dai kama Hama ne a shekarar da ta gabata, bisa zargin yana da hannu a badakalar sayen Jarirai daga makwafciyar kasar, Najeriya .

Hama ya sha musanta zargin.

Hama tsohon kakakin majalisar dokokin Nijar ya ce zarge-zargen da ake masa makarkashiyar siyasa ce, ya kuma zargi Shugaba Muhammadou Issoufou da daukar tsauraran matakai a kan 'yan hamayya gabannin zaben kasar.

A karshen makon jiya ne dai aka tabbatar da Hama Amadou a cikin 'yan takara 15 da za su fafata a zaben shugaban kasa.