Borno: wasu 'yan gudun hijira sun koka

Image caption yan gudun hijira najeriya

A jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, 'yan gudun hijira da dama da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu na kokawa da halin da suke ciki.

Rashin tallafin abinci da ruwan sha da saura abubuwan more rayuwa daga hukumomi na daga cikin abubuwan da suke damunsu.

Galibinsu dai yanzu haka na zaune ne a sansanoni daban-daban da gwamnati ta tanada a cikin Maiduguri babban birnin jihar.

Sai dai kuma hukumomin na cewa suna bakin kokarinsu wajen ganin cewa yan gudun hijirar sun samu kulawa yadda ya kamata.

Ganin cewa an fara samun yanayin tsaro mai kyau a wasu yankunan jihar ta Borno wasu daga cikin yan gudun hijirar na cewa da a maidasu garuruwan da suka fito.