An mika tutar karshe ga sojojin Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tchad Army

Kwamandan rundunar sojojin hadin-gwiwa ta kasashen yankin tafkin Chadi ya shugabanci bikin mika tuta ga sojojin kasar Chadi.

An gudanar da wannan bikin mika tutar ne a garin Baga-Sola da ke cikin yankin tafkin Chadi.

Wannan mika tuta wadda ta ita ta karshe , da Kwamandan rundunar ya yi.

Daukacin sojoji sama da 8,000 sun shiga karkashin kulawar rundunar hadin gwiwa.

A halin yanzu dai sojojin sun fita daga karkashin tutocin kasashensu.