Wani babban dan sandan China zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu Li Dongsheng da laifin karbar hancin sama da dala miliyan uku.

Hukumomi a kasar China sun yanke hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari kan wani tsohon mataimakin shugaban 'yan sandan kasar bayan an same shi da karbar hanci.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce wata kotu a birnin Tianjin ta samu Li Dongsheng da laifin karbar hanci.

Masu shigar da kara sun zarge shi da karbar hancin sama da dala miliyan uku da yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Mista Li makusanci ne ga tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar, mai karfin fada-a-ji, Zhou Yongkang - wanda shi ne babban jami'in da gwamnatin Shugaba Xi Jingping ta samu da karbar hanci da rashawa.

An daure shi ne a watan Yunin da ya wuce.