Iran ta saki jiragen yakin Amurka

Image caption Jirgin ruwan yakin Amurka

Rundunar sojojin kundumbalar Iran ta ce ta saki jiragen yakin Amurka na ruwa biyu wadanda ta kama bayan sun yi kutse a tekun Iran.

Jiragen suna dauke ne da ayarin matuka goma.

Wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Iran ta ce an saki jiragen ne bayan Amurka ta bayar da hakuri a kan kutsen da suka yi.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Amurka ke son Iran ta aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla da ita game da dakatar da sarrafa makamashin nukiliyarta.

Sanarwar ta kara da cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa jiragen sun shiga yankin da ke karkashin ikon Iran ne bisa kuskure.

Amurka dai ta ce jiragen ruwan na atisaye ne a teku, tsakanin Kuwait da Bahrain sai daya daga ciki ya lalace, kuma daga nan ruwa ya ja shi zuwa yankin da ke karkashin ikon Iran.