Kananan likitoci na yajin aiki a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto

Dubun dubatar kananan likitoci na Ingila sun fara yajin aiki na sa'oi 24 a kan albashi da wasu hakokkinsu.

Gwamnati tana so ta fitar da sababbin sharuda da za su kai ga kara wa likitocin albashi amma za ta rage yawan kudaden da take biyansu idan suka yi aiki a lokutan da ba safai suke yi ba, wato kamar aiki dare da aiki a karshen mako.

Likitocin sun nuna rashin amincewarsu da hakan inda suka ce ba a yi musu adalci ba, kuma hakan ka iya jefa marasa lafiya a cikin hadari.

A lokacin da suke gudanar da yajin aikin, likitocin za su kula da masu bukatar agajin gaggawa ne kawai.

Yajin aikin ya sa an dakatar da tiyata da aka saba yi da kuma wasu abubuwan da suka dangancin hakan.

Firai Ministan Biritaniya, David Cameron, ya ce yajin aikin zai yi illa ga harkokin kiwon lafiya a