Taliban ta jefa mazauna Helmand cikin zulumi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Lashkar Gah shi ne babban birnin lardin kuma yana hannun gwamnatin kasar.

Sai dai akasarin yankunan lardin, wanda ya yi kaurin-suna wajen fadace-fadace saboda kasancewarsa cibiyar safarar miyagun kwayoyi, yana hannun masu tayar da kayar-baya.

Abokaina da dama da ke ci gaba da zama a Lashkar Gah suna tunanin ficewa daga cikinsa.

A baya dai muna jin dadin zuwa gefen ruwan Helmand river, da kallon rana idan za ta fadi da shan kayan marmari da kuma yin hira.

Haka kuma muna tattaunawa a kan sababbin motocin da aka kera ko kuma zuwa hutu kasashen waje.

Amma yanzu muna tunanin yadda za mu tsere daga yankin ne.

Mutane na cikin shiri ko da 'yan kungiyar Taliban za su zo.

Sai dai ficewa daga garin ba abu ne mai sauki ba: saboda abokaina sun yi aure, sun gina gidaje, sannan suna gudanar da kasuwanci.

'Zaman zulumi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Reuters

Al'amuran da ke faruwa a Sangin, wanda bai wuce kilimota 100 tsakaninsa da yankin ba, ya jefa mutanen Lashkar Gah cikin zaman-zulumi.

An kashe sojojin Biritaniya da dama a shekara takwas da 'yan kungiyar Taliban suka kwashe suna cin karensu babu babbaka a yankin.

Shi kansa lardin Helmand yana fuskantar matukar hatsari.

Hakan na faruwa ne kuwa saboda dakarun tsaron Afghanistan ba su da karfi a lardin, sannan 'yan Taliban sun kankane ko'ina.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Masu sukar gwamnati sun ce ta kasa karfafa jami'an tsaro a lardin saboda karbar hanci da rashawa da kuma rashin sadarwa mai inganci, suna masu cewa hakan ya kara wa 'yan Taliban karfi.

Wani kwamandan kungiyar Taliban ya shaida wa BBC cewa suna sayen akasarin makamansu ne daga hannun jami'an tsaron Afghnaistan.

Ko da ya ke babu wata kafa da ta tabbatar da wannan ikirarin, amma dai an lura cewa 'yan kungiyar suna yin amfani da wasu makamai irin na dakarun tsaro.

Sai dai gwamnan Helmand Mirza Khan Rahimi, ya musanta zarge-zargen da ake yi cewa sun kasa shawo kan matsalar tsaron yankin.

'Rudani'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban rundunar 'yan sandan Helmand Abul Rahman Sarjang ya sha suka sosai.

Sunansa dai na nufin "gwarzo a wajen yaki", kuma a jawabinsa na farko bayan ya karbi mukamin, ya ce zai tabbatar ya murkushe masu tayar da kayar baya.

Sarjang ya ce, "Ban zo nan domin na zauna lafiya da 'yan Taliban ba. Na zo ne domin na yi yaki da su."

Mazauna birnin sun yi ta zolayarsa saboda kalaman nasa, musamman bayan 'yan Taliban sun fatattaki jami'ansa lokacin da suka yi yunkurin kai musu farmaki.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Al'amuran tsaro sun ci gaba da rincabewa, musamman a Sangin, inda aka katse hanyoyin da sojojin Afghanistan ke bi domin kai wa mutane dauki.