Aljazeera za ta rufe ofishinta na Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Talabijin na Aljazeera

Gidan Talabijin na Aljazeera ya sanar da cewa zai rufe ofishinsa da ke Amurka, kasa da shekara uku da budewa.

Gidan Talabijin din ya ce zai daina gabatar da shirye-shiryensa a Amurka ne a karshen watan Afrilu mai zuwa saboda yanayin da ya samu kansa a Amurka.

A cewar gidan Talabijin din yanzu zai mai da hankali wajen fadada ayyukansa ta kafafen internet.

Wakilin BBC ya ce gidan Talabijin din ya gaza wajen samun isassun abokan hulda ta yanda zai samu kasuwa mai armashi a Amurka.