Karin dakarun Biritaniya za su je Nigeria

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dakarun Biritaniya na yaki da Taliban

Karin dakarun Biritaniya 35 ne ke shirin zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

A watan da ya wuce ne sakataren tsaron Biritaniya, Micheal Fallon ya bayyana cewa kasar za ta ninka yawan dakarunta a Najeriya zuwa 300 domin bayar da taimakon soji.

"Za mu ci gaba da hada kai da Najeriya domin murkushe 'yan Boko Haram," in ji Fallon.

A shekarar da ta wuce ne, Biritaniya ta aika dakaru 130 zuwa Najeriya domin soma gudanar da horon.

Kawo yanzu dai an horas da dakarun Najeriya fiye da 1,000 a cikin shirin da gwamnatin Biritaniya ke daukar nauyi.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.