Fastoci sun shawarci Buhari kan yaki da rashawa

Image caption Buhari ya sha alwashin yaki da karbar hanci da rashawa.

Manyan limaman cocin Ebanjelika na Najeriya sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya daina bata lokacinsa wajen yaki da mutanen da suka sace kudin kasar.

Limaman sun ce yin hakan zai dauke masa hankali daga aiwatar da ayyukan ci gaban kasar.

Daya daga cikinsu, Pasto Matthew Ashimolowo, ya ce, "Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya, wanda ke son bai wa kasar abin da take so. Amma idan ya bata lokaci wajen kama manyan barayi, yawancinmu da ba mu yi sata ba za mu sha wuya".

Ya kara da cewa dole ne Shugaba Buhari ya rika sara yana duban bakin gatari ta yadda 'yan kasar za su ci gajiyar mulkinsa.

Hukumomin da ke yaki da karbar hanci da rashawa dai sun kama manyan jami'an gwamnatin da ta gabata bisa zarginsu da hannu a wajen karbar hanci da rashawa.