Gwamnatin Romania ta yi amai ta lashe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnati ta ce ce an fara wuce-gona-da-iri wajen cin gajiyar dokar.

Gwamnatin Romania ta ce za ta yi wani sauyi ga wata dokar kasar da ta bai wa fursunoni damar rage wa'adin zamansu a gidan-kaso idan suka wallafa littafi.

Wadanda aka daure za su iya rage daurin da wata guda idan suka wallafa wani aikin da suka yi a kan adabi ko kimiyya.

Ministan Shara'ar kasar ya ce an fara wuce-gona-da-iri wajen cin gajiyar dokar, don haka ne aka sauya dokar da wata doka ta gaggawa.

Ana rage wa masu zaman gidan yari watanni masu yawa gwagwadon litattafan da suka wallafa.

Cikin fursunonin da aka saki da wuri har da tsohon Firayim Ministan kasar, Adrian Nastase, wanda ya wallafa wasu litattafai a kan cin hanci da rashawa lokacin da yake tsare.