Rabin yaran Sudan ta Kudu ba sa zuwa makaranta

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya ta ce sama da rabin yara a Sudan ta kudu ba sa zuwa makaranta saboda rikici.

Hukumar ta kara da cewa yawan yaran da ba sa zuwa makarata a Sudan ta kudun ya zarta na ragowar kasashe.

Dakarun gwamnati sun shafe shekara biyu suna fafatawa da 'yan ta'adda, ko da ya ke an sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a cikin watan Agusta.

Nijar ce kasa ta biyu, inda kashi 47 cikin dari na yaran kasar ba sa zuwa makaranta, yayin da kasar Sudan ke da kashi 41 da kuma kasar Afghanistan da kaso 40 cikin 100.

Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya ta ce, yara miliyan 24 na cikin sama da yara miliyan 109 da suke rayuwa a kasashen da ake yaki ba sa zuwa makaranta.

Hukumar ta kara da cewa da ma kafin somawar rikicin, yara miliyan daya da dubu dari hudu sun bata a Sudan ta kudu.