Jirgin Yaki: Amurka ta gode wa Iran

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Dakarun Amurka da Iran ta sako

Amurka ta gode wa Iran game da sakin matuka girginta su 10, kwana daya bayan da aka kama su a yankin ruwan Iran din.

Sakataran harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce warware matsalar cikin ruwan sanyi da hanzari ya nuna irin rawar da diflomasiyya ke takawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta musanta ikirarin da Iran ta yi na cewa Mr Kerry ya ba su hakuri.

Dakarun sojin Iran sun ce sun yadda cewa ba da gangan ba ne suka shiga yankin ruwan kasar ranar Talata.

Masu aiko da rahotanni sun danganta hanzarin da Iran ta yi na warware matsalar da cewa ana saran nan da 'yan kwanaki kasashen yamma za su dage takunkumin tattalin arzukin da suka sakawa Iran din.