Kotu ta bayar da umarnin kama Tompolo

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Ana zargin Tompolo ne da yin sama-da-fadin Naira biliyan talatin da hudu.

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Legas na Najeriya ta bayar da sammacin kama tsohon madugun 'yan fafutikar kwato 'yancin Naija Delta, Mista Government Ekpemupolo Tampolo domin gurfana a gabanta.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ce ta shigar da kara a kan zarginsa da kuma Patrick Akpobolokemi tsohon manajan daraktan hukumar kiyayewa da samar da tsaro a gabar tekun Najeriya, NIMASA, wajen hada baki domin sace kimanin naira biliyan 34 da sunan sayen fili. Sai dai Tompolo ya ki gurfana a gaban kotun, kuma alkalinta, mai shari'a Ibrahim Buba, ya bayar da sammacin kamo da kuma gurfanar da Tampolo a gaban kotun.

Tsohon manajan daraktan hukumar NIMASA dai ya gurfana a gaban kotun yana dingishi, kuma rike da kwagiri da ke nuna alamun yana da rauni a kafarsa .

Ana zargin Tompolo da kuma tsohon manajan daraktan NIMASA da laifuka 40 wajen hada baki da safarar kudade ta haramtacciyar hanya da suka kai naira biliyan 34 da sunan damfara bayan cimma wata yarjejeniya a tsakanin NIMASA da kuma kamfanin Global West Vessel Limited, mai kula da harkar tsaron teku.

EFCC ta kuma gurfanar da wasu mutanen hudu Kime Engozu, Rex Elem, Gregory Mbonu da Kyaftin Warredi Enisuoh wadanda take zargi da hada baki da su Tompolo wajen sace kudin.

Tompolo dai makusancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne.