Kasa da fursunoni 100 suka rage a Guantanamo

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption A Guantanamo ne Amurka ke tsare manyan fursunoni

Amurka ta mayar da wasu fursunonin Yemen guda 10 daga gidan yari na Guantanamo Bay zuwa kasar Oman.

Za su ci gaba da kasancewa a Oman har sai al'amura sun daidaita a Yemen.

'Yan kungiyar Houthi mabiya Shi'a suna yaki da gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka yarda da ita bayan sun kwace ikon mafi yawan bangarorin kasar.

Yanzu dai fursunoni kadan ne suka yi saura a gidan yarin Guantanamo.

Wannan sakin, shi ne mafi yawa na fursunoni a Guantanamo tun lokacin da shugaba Obama ya karbi mulki.

Ya yi alkawarin rufe gidan yarin, tun a wa'adin mulkinsa na farko.