Za a yi wa 'yan sandan Nigeria gwajin kwakwalwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin wasu 'yan sanda da laifin kisan gilla a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da umurnin a yi wa dukkan 'yan sandan da ke rike da makamai gwajin kwakwalwa.

Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce manufar yin hakan ita ce a tabbatar da cewa suna da cikakken hankali wajen gudanar da ayyukansu.

Kakakin 'yan sandan, ACP Olabisi Kolawole wacce ta sanya wa sanarwar hannu, ta ce sufeto janar Solomon E. Arase ya dauki wannan matakin ne saboda a magance matsalar saba kai'da wajen yadda wasu 'yan sanda ke amfani da bindiga.

A cewar kakakin, aikin 'yan sanda shi ne kare rayukan al'umma, ba wai kashe mutane babu gaira babu dalili.

Mista Arase ya umarci dukkan likitocin 'yan sanda a kasar su gudanar da gwajin kwakwalwa kan 'yan sandan da ke rike da makamai sau hudu a shekara, saboda tabin kwakwala na iya bata sunan rundunar 'yan sandan kasar.