An kawar da Ebola daga yammacin Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ebola ta kashe mutane sama da dubu 11

Hukumar kula da lafiya ta duniya, WHO ta ayyana yammacin Afirka a matsayin yankin da ya kubuta daga cutar Ebola.

Hukumar, wacce ta bayar da sanarwar ranar Alhamis, ta kara da cewa Laberiya, wacce ita ce kasa ta karshe da ta kawar da cutar, ta tsira daga sharrin Ebola.

Sai dai WHO ta ce ya kamata a sanya idanu sosai domin ganin cutar ba ta sake barkewa a yankin ba.

Laberiya ce kasa ta farko da aka ayyana a matsayin wacce ta kawar da cutar a watan Mayu na shekarar 2015, sai dai tun daga wancan lokacin mutane biyu sun sake kamuwa da ita.

Sai dai sanarwar ta yau ta biyo bayan kwashe kwana 42 da aka yi a kasar ba tare da an samu wanda ya kamu da cutar ba.

Babban jam'in WHO a Laberiya, Dr Alex Gasasira, ya ce "Muna bai wa mutane shawara da su kula sosai da lafiyarsu sannan su yi gaggawar sanar da hukumomin lafiya idan suka ga alamun cutar".

Ebola dai ta fi yin barna a kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea, inda ta kashe mutane da dama.