El-Zakzaky ya gana da majalisar koli ta addinin Musulunci

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana cewar ta gana da Sheikh Ibrahim El-zakzaky da uwargidansa a inda suke tsare.

Daya daga cikin mambobin majalisar, Farfesa Dahiru Yahaya wanda ke cikin tawagar da ta gana da ElZakzaky, ya shaida wa BBC cewar, shugaban na 'yan Shi'a ya soma murmurewa daga harbin bindiga da aka yi masa.

Tuni kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement a Najeriya ta yi maraba da wannan matakin, inda ta kara yin kira a sako jagoranta, Sheikh El-Zakzaky da sauran 'yan kungiyar da ake tsare da su.

Tun a cikin watan Disamba jami'an tsaro suka kama El-Zakzaky bayan rikici tsakanin mabiyansa da sojoji a Zariya.

Ga hirar Abdullahi Tanko Bala da Farfesa Dahiru Yahaya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti