An tsare Metuh a gidan yarin Kuje

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Sai a mako mai zuwa za a ci gaba da sauraron karar Metuh

Babbar kotun tarayya a Abuja, ta ba da umurnin a tsare kakakin jam'iyyar adawa ta PDP, Mr Olisa Metuh a gidan yari na Kuje.

Kotun ta ce a ci gaba da tsare Metuh har zuwa ranar 19 ga watan Janairu, kafin a duba batun bayar da belinsa.

Hukumar EFCC ce ta kai shi gaban kuliya bisa zargin ya karbi Naira miliyan 400 daga hannun, Kanar Sambo Dasuki a cikin kudin makamai da ake zargin sun karkatar da su.

Mr Metuh ya musanta zargin.

EFCC na tuhumar 'yan siyasa da dama bisa zargin wawure kudaden siyo makamai karkashin jagorancin, tsohon mai bai wa shugaba Jonathan shawara ta fuskar tsaro, Kanar Dasuki mai ritaya da suka kai dala biliyan biyu da wani abu.