EFCC za ta binciki tsofaffin sojoji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Badeh na daga cikin wadanda za a bincika

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a binciki wasu tsofaffin hafsoshin sojojin kasar bisa zarginsu na hannu wajen wawure kudaden gwamnati na sayen makamai.

Ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa daga fadar shugaban kasa inda ya bayar da umarnin hukumar da ke kula da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC su yi bincike kan tsofaffin sojoji, da kuma wasu jami'an soji masu ci yanzu da kuma wasu kamfanoni jimilla 40 da ake zarginsu da hannu a badakalar sayen makamai.

A cikin jerin sunayen wadanda ake zargin, har da tsofafin manyan hafsoshin sojojin sama da kasa na Najeriya, wadanda su ka yi aiki a karkashin tsohon shugaba, Goodluck Jonathan.

A rahoto na farko da kwamitin bincike kan sayen makamai ya fitar, ya ce an kashe dala biliyan biyu da miliyan dari daya wajen sayen makamai a shekarar 2015.

Rahoto na biyu kuma ya gano cewa an kashe Naira biliyan 29 da kuma dala biliyan biyu wajen sayen kayayyakin sojin sama.

Ga jerin sunayen wadanda za a bincika:

 • Air Chief Marshal AS Badeh (Rtd)
 • Air Marshal MD Umar (Rtd)
 • Air Marshal AN Amosu (Rtd)
 • Maj-Gen. ER Chioba (Rtd)
 • AVM IA Balogun (Rtd)
 • AVM AG Tsakr (Rtd)
 • AVM AG Idowu (Rtd)
 • AVM AM Mamu
 • AVM OT Oguntoyinbo
 • AVM T Omenyi
 • AVM JB Adigun
 • AVM RA Ojuawo
 • AVM JA Kayode-Beckley
 • Air Cdre SA Yushau (Rtd)
 • Air Cdre AO Ogunjobi
 • Air Cdre GMD Gwani
 • Air Cdre SO Makinde
 • Air Cdre AY Lassa
 • Col N Ashinze
 • Lt Col. MS Dasuki (Rtd)