Habro ya kera abin debe wa tsofaffi kewa

Image caption Jim da Alan,na raha.

Kamfanin Habro mai kere-keren kayan wasa ya kera samfurin butum-butumin kyanwa don amfani wajen debe wa tsofaffi da masu fama da cutar mantuwa ko kadaici kewa.

Jim McGucken wani mazaunin gidan kula da tsofaffi ne a Lake Park da ke birnin Oakland na jihar California.

Alan shi ne sunan da ya lakabawa butum-butumin kyanwar.

Jim ya ce yana jin kamar wata kyanwa ce mai rai a jikinsa lokacin da ya rungume Alan.

Ya nuna farin cikinsa da wannan sabuwar fasaha da ya ce ta sauya masa rayuwa matuka.

Fasaha

An kera butum-butumin kyanwar ne ta yadda za ta rika kwaikwayon yadda dabba mai rai ke yi.

Takan yi kuka tare da yin duk wasu dabi'u irin na kyanwa.

Gashin jikinta na da tafshin gaske, duk kuwa da cewa na'urorin da aka dasa a cikin ta na saurin ganar da mutum cewa ba mai rai ba ce.

Za ka iya sarrafa mutun-mutumin kyanwar ta hanyar amfani da wasu wayoyi masu sansano motsi da ke kewaye da jikinta.

Ga misali idan aka yi wa Alan cakul-kuli a kumatu ta zata yi kukan kyanwa, idan aka shafa bayan ta kuma za ta rika gurnani, idan kuma duhu ya yi za ka ga Alan na hamma na gyangyadi.

"Ba ma jin wannan zai maye gurbin dabbar gida, '' in ji Ted Fitcher, mataimakin jagoran kamfanin na Hasbro.Kuma an yi arashi ba ya son mu'amala da mage.

Image caption Paro, butum-butumin dorinar ruwa, an yi masa caji da wuta.

Yayin da yawan al'umma ke karuwa a duniya, kamfanin na Hasbro na kara samun bunkasa da kuma dama a kasuwancinsa.