'Sojojin Burundi suna yi wa mata fyade'

Hakkin mallakar hoto reuters

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ya ce yana da shaida da ke nuna cewa dakarun tsaron Burundi suna taruwa su yi mace guda fyade a lokacin da suke neman wadanda ake zargi da goyon bayan 'yan adawa.

Zeid Raad al Hussein ya ce a lokacin da suka gudunar da binciken, dakarun tsaron sun sace da azabtar da kuma kashe matasa da dama.

Ya kara da cewar cin zarafin ya auka ne bayan harin 'yan ta'adda a tsakiyar watan Disamba a sansanin sojoji guda uku.

Al Hussein ya kara da cewa ana kuma zargin akwai kaburuka masu yawa.