Amurka ta hana masu ciki zuwa kasashe 17

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'an lafiya a Amurka sun shawarci mata masu juna biyu a kasar da kada su yi tafiya zuwa wasu kashe 17 na Latin Amurka da Karebiya, wadanda aka samu cutar zazzabin cizon sauro ta Zika a cikinsu.

Ana ta'allaka karuwar haihuwar yara da nakasa a jiki da ake yi a Brazil, akan barkewar cutar ta Zika.

A watan Oktoban 2015, ma'aikatar lafiya a Brazil din ta fara samun rahotannin yawaitar haihuwar yara da kananan kawuna, da kuma rashin cikakken hankali.

Kawo yanzu, an samu yara fiye da 3500 da aka haifa a Brazil din dauke da cutar zazzabin na Zika, kuma akalla yara 38 ne suka mutu sakamakon cutar zuwa yanzu.