Mutane 29 suka mutu a harin Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Reuters

Karin bayanai sun bayyana game da harin da masu kishin Islama suka kai ranar juma'a a kan wani otel da wani wurin shan shayi a Wagadugu babban birnin Burkina Faso.

Mutane akalla 29 ne dai aka kashe, galibinsu a wurin shan shayin.Wani mai aiko wa BBC labarai a Burkina Faso ya ce jerin sunayen wadanda lamarin ya shafa da kawo yanzu aka gane ko suwa nene ne sun hada da mutane daga wasu kasashe daban daban har 9.

Akwai dai yan Canada da Amurkawa da kuma yan Libya a cikin wadanda suka mutu din.Ya ce rahotannin farko cewar biyu daga cikin yan gwagwarmayar mata ne, ba daidai ba ne , saboda an gano dukaninsu maza ne.

A halin yanzu kuma kasar Australia ta ce tana aiki tare da hukumomin Burkina Faso domin kokarin samun sakin wasu tsaffi miji da mata da wadanda ake zargin masu kishin islamar ne suka yi garkuwa da su a arewacin kasar.