'Mune muka kai hari a Burkina Faso'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

"Tushen Al-Qa'ida a Afrika"

Kungiyar AQIM wadda ta dauki alhakin kai harin, ta samo asali ne tun yakin basasar da aka yi a Aljeriya a shekarun 1990.

Kungiyar ta kafu ne daga wasu dakarun 'yan tawaye da ke samun kudin shigarsu daga sace Turawa da fataucin makamai da kwayoyi.

A shekarar 2007 ta sanar da yin mubaya'arta ga babbar kungiyar Al-Qa'ida domin ta yaki kasashen yamma.

Amma daga baya wasu daga cikin mayakanta sun balle inda suka kafa ta su kungiyar.

Shahararru daga cikinsu su ne Mokhtar Belmokhtar, wanda shi ne kashin bayan kawanyar da aka yi wa kamfanin iskar gas na Aljeriya a shekarar 2013.

Kawunan kungiyar AQIM ya rarrabu a sassa daban-daban na arewacin Afrika da kuma yankin Sahel.

Amma a watan Nuwambar 2015, bangaren Belmokhtar ya ce yana aiki ne da babbar kungiyar ta Al-ka'ida inda suka kai hari kan wani otal a Mali.

Wannan hari na Burkina Faso wani kokari ne na AQIM ba wai kawai don ta karfafa kanta a matsayin babbar kungiyar jihadi ta Afrika ba, sai don ta kuma nuna cewa a shirye take ta watsa akidarta ga sauran sassan yankin.