An cire wa Iran takunkumi

Image caption Shugaban Iran Hassan Rouhani

An dage takunkumin kasa da kasa da aka sanya wa Iran, lamarin da yanzu, zai ba kasar damar ci gaba da juya kadarorin ta da aka rike masu darajar kudi dala biliyan dari, da kuma samun damar shiga kasuwannin mai na duniya.

An bayar da sanarwar dage takunkumin ne a birnin Vienna, inda hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa Iran din ta cika nata alkawarin yarjejeniyar da aka cimma da ita, akan takaita sarrafa sinadarin nukiliya.

Sai dai, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce duk da cewa Iran din ta rage barazanar da take na kera makamin kare dangi, ya zama wajibi a ci gaba da sa mata ido.

Kazalika, yayin da kasashen duniya ke murna da nasarar da aka samu, Isra'ila ta ce har yanzu Iran din na son ta mallaki makamin kare dangi.

A Amurka ma, kakakin majalisar dokokin kasar dan jam'iyyar Republican ya ce akwai yiyuwar Iran din ta yi amfani da rangwamen da ta samu wajen daukar nauyin ayyukan 'yan ta'adda.

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya yi marhabin da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da kasar ta sa, yana mai cewa dage takunkumi da dama aka sanya ba bisa ka'ida ba, zai kawo ci gaba ga kasarsa.