Takunkumin da aka sanyawa Iran ya zo karshe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, ya ce a ranar Asabar ne za a dage takunkumin da kasashen duniya suka sanyawa kasarsa.

Mista Zarif ya fadi hakan ne bayan isar sa Vienna inda zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

Ana sa ran hukumar da ke sa ido kan makamin Nukiliya ta duniya IAEA, za ta fitar da wani rahoto da zai tabbatar da cewa Iran ta rage wasu burika na harkar nukiliyarta, kamar yadda ta sanya hannu a yarjejeniyar da aka cimma cewa shirin nukiliyar zai mayar da hankali ne kan al'amuran zaman lafiya kawai.

Hadin kan da Iran ta bayar zai bata damar damun biliyoyin daloli na kadarorinta da kuma fara sayar da man fetur dinta a kasuwannin duniya.