Iran ta sako Fursunoni hudu 'yan Amurka

Jason Rezaian Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jason Rezaian

Iran ta sanar da sakin fursunoni hudu masu ruwa biyu wadanda ke da shedar 'yan kasa na Iran da kuma Amurka.

Wannan dai na daga wani shirin musayar fursunoni a tsakanin kasashen biyu.

Ana tsammanin sun hada da dan Jaridar Washington Post Jason Rezaian wanda aka daure bisa zargin leken asiri a Iran a bara.

Hakan nan kuma an bada rahoton sakin wani Pastor Saeed Abedini.

Babban lauyan gwamnatin Iran yace sakin mutanen wani tsari na musayar fursunoni kuma an yi shi ne bisa alfanunsa ga kasa.

Sanarwar ta zo ne yayin da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Iran Javad Zarif suke ganawa domin tattauna dage takunkumin da kasashen duniya suka kakabawa Iran din.