"Mun ji dadi da juyin mulkin farko a Najeriya"

Hakkin mallakar hoto Getty Keystone France Gamma Keystone

Yayin da ake ci gaba da alhinin cika shekaru hamsin da juyin mulkin farko a Nigeria, wasu 'yan jam'iyyar adawa ta NEPU a kasar a wancan lokaci, cewa su ka yi, su kam, sun yi farin ciki da juyin mulkin, domin ya kawo musu 'yancin walwala da suka rasa, a lokacin gwamnatin NPC.

Alhaji Lili Gabari na jam'iyyar NEPU, ya ce juyin mulkin ya faru ne a kan gaba, a don haka, ya ce sun yi farin ciki da juyin mulkin.

Ya yi zargin cewa kafin juyin mulkin ya faru, talakawa suna cikin ukuba, sannan ana bayar da bashin noma, da daukan aiki ne ta la'akari da alfarma.

Kazalika, Alhaji Gabari ya yi zargin cewa kafin juyin mulkin, Najeriya tana cikin rashin tabbas, amma juyin mulkin ya sa an kawar da wasu mutane da suka hana ruwa gudu.

Ya ce 'yan NEPU sun yi murna da juyin mulkin, inda ya ce Allah ya kawo musu karshen ukubar da suke ciki da suka hada da dauri, da hana su sana'a.