Jami'an Custom za su bayyana kadarorinsu

Hakkin mallakar hoto Custom
Image caption Shugaban hukumar Custom, Kanal Hamid Ali mai ritaya.

Dukkan jami'an fasa kwauri na Najeriya Custom, za su fara bayyana kadarorin da suka mallaka, a wata sabuwar hanya ta magance cin hanci da rashawa da kuma bin tsarin doka.

Umarnin bayyana kadarorin na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban hukumar Custom din Kanal Hammed Ibrahim Ali mai ritaya, ya sanyawa hannu, wadda aka aikewa dukkan mataimakansa da ke shiyyoyin kasar.

Sanarwar ta kuma umarci dukkan jami'an da su cika wannan sharadi cikin kwanaki 14.

Tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki ne hukumomi daban-daban na kasar suke daukar matakai don hana cin hanci da rashawa.