"Jami'an Custom sun kashe mana fasinja"

Hakkin mallakar hoto NCS
Image caption 'Yan kasuwa sun koka kan jami'an custom

Wasu 'yan kasuwa da direbobin manyan motoci da ke safara a tsakanin titin Lagos da Shagamu zuwa arewacin Najeriya, sun koka a kan yadda jami'an custom masu sintiri a wannan shiyya ke cin zarafinsu.

Wannan kuka nasu ya zo ne sakamakon zargin da direbobin su ka yi cewa wasu jami'an custom sun harbe daya daga direbobinsu har lahira da kuma jikkata wani fasinjan da yanzu haka yake cikin mawuya cin hali.

Masu motocin sun ce suna kan hanyarsu ne ta zuwa Jos don kai wasu kaya, kuma sun ce ba sa dauke da wani haramtaccen abu da zai sa jami'an custom din su yi musu haka.

Hukumar custom reshen jihar Ogun, ta ce bata da labarin wannan al'amari, amma tana nan tana neman bayanai daga bakin jami'an da aka dorawa alhakin yin sintiri a yankin.