'Ba laifi a yi wa kasafin kudi garanbawul'

Image caption Honoroble Kawu Sumaila ya ce an samu sauye-sauye a kudurin kasafin kudin

Wasu jami'an gwamnatin Najeriya sun ce ba laifi ba ne idan shugaba Muhammadu Buhari, ya yi wa kudirin kasafin kudin da ya gabatar na shekarar 2016 ga majalisar dokokin kasar garanbawul.

Jami'an sun ce kazalika, su ma 'yan majalisa suna da iko, bisa tanadin da kundin tsarin mulkin kasar yayi, na yi wa kudurin kasafin gyara.

A tsakiyar makon da ya gabata ne dai majalisar dattawan kasar ta yi zargin cewa takardun kasafin kudin da ke zauren ta a halin yanzu, sun banbanta da na farko da shugaba Buhari ya gabatar ma ta a watan Disambar bara.

Kawu Abdurrahman Sumaila, mai ba wa shugaba Buhari shawara ne kan al'amuran majalisar wakilan kasar, kuma a hirar da ya yi da wakilin BBC Usman Minjibir, ya ce an samu 'yan sauye-sauye a kudurin, sai dai ya ce sauye-sauyen ba su shafi gundarin kudin kasafin ba na Naira tiriliyan shida da digo takwas ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti