Ana fama da matsanancin yunwa a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, mutane dubu dari biyu a Syria na fama da matsanancin karancin abinci a birnin Deir al-Zour da ke gabashin kasar, inda mayakan kungiyar IS suka kaddamar da sabbin hare-hare kan wasu gundumomi dake karkashin ikon gwamnati.

Majalisar ta ce ta samu wasu rahotanni da ba a tantance su ba, da ke nuna cewa mutane 20 sun mutu saboda yunwa.

Kungiyar ta IS ce ke rike da iko da kusan baki daya birnin na Deir al-Zour, kuma ta ci gaba da yin kawanya a wasu sassan yammacin birnin, wata da watanni.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Syrian ya ce akalla fararen hula dari uku ne aka kashe a harin.