An kai harin kunar bakin wake Afghanistan

Mayakin Taliban Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Taliban sun sha kaddamar da hare-hare a Afghanistan.

Akalla mutane goma sha daya ne suka rasa rayukansu ya yin da wani dan kunar bakin wake ya tada bam a kusa da gidan wani fitaccen dan siyasa da ke birnin Jalalabad a Afghanistan.

A kwanakin baya ne mayakan Taliban suka saki dan Obaiduallah Shinwari da sukai garkuwa da shi, mutane sun taru a gidan dan taya shi murnar a lokacin da aka tashi bam din.

Mr Shinwari ya ji mummunan rauni, ya yin da dan na sa ya rasu nan take tare da wasu mutanen da kuma wadanda suka jikkata.

Sai dai mayakan Taliban sun musanta kai harin.