An sace Amurkawa da dama a Iraqi

Image caption Taswirar birnin Bagadaza da ke kasar Iraki.

Ofishin huddar jakadancin Amurka a Iraqi, ya tabbatar da cewa an sace Amurkawa da dama a Bagadaza, babban birnin Irakin.

Jami'an sun ce suna aiki tare da hukumomi a Iraki a yunkurin nemo mutanen, sai dai basu yi karin bayani ba dangane da adadin mutanen da suke nema.

Wani wakilin BBC a can ya ce an sace 'yan Amurkawan da dama amma ba a san addadin yawan su ba, duk cewa daga farko dai gidan talabijin din kasar Al Arabiya, ya bayar da rahoton cewa an sace 'yan Amurka guda uku a Iraki."

Wasu rahotannin daga jami'an tsaro na Iraqin da ba a tabbatar ba kuma, sun ce an sace Amurkawa uku da wani tafintan Amurkar a wata unguwa da ke kudancin birnin Bagadaza.

Kana wani jami'in gwamnati a birnin Bagadaza ya shaidawa kafar yada labarai ta CNN cewa wasu 'yan kwangila Amurkawa uku sun yi batan dabo a ranar Jumma'a.

A ranar Lahadi ne wani kamfani ya bayar da rahoton cewa uku daga cikin ma'aikatansa Amurkawa sun bata kwanaki biyu da suka gabata.

Kafin ficewar dakarun Amurka daga kasar Iraqi a shekara ta 2011, kungiyoyin masu rike da makamai na Shi'a da kuka Sunni sun sace yan kasashen yammacin duniya da dama.

Ko a cikin watan da ya gabata ma an sace wasu mafarauta 'yan Qatar a cikin saharar kasar ta Iraqi, da suka hada da 'yan gidan sarauta.