An cire wa Iran takunkumi

Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana kai ruwa rana kan batun dage takunkumin.

Shugaba Hassan Rouhani yace dage takunkumin da aka kakabawa kasarsa, ya bude sabuwar hanyar alaka tsakanin Iran da kasashen duniya.

Mr Rouhani ya na yin wannan jawabi ne a majalisar dokokin kasar, bayan da masu sanya ido kan makamin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya su ka tabbatar da cewa Iran ta takaita kera makamin nukiliyarta, wanda hakan ya sa aka dage takunkumin da aka kakaba ma ta.

Mr Rouhani ya kara da cewa al'umar kasar na cike da farin ciki da wannan mataki, sai dai 'yan tsiraru da ba sa farin ciki da hakan irin kasar Israela da wasu daga cikin 'yan majalisar Amurka.

Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace barazanar Iran ta kera makamin nukiliya ta ragu matuka, amma duk da haka za a ci gaba da san ya idano akan ta.