IS sun hallaka mutane 300 a Syria

Wani dan IS Hakkin mallakar hoto isis video
Image caption Matasa da dama ne suka shiga kungiyar IS.

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria ya rawaito cewa mayakan IS sun hallaka fararen hula 300 a wani kauye da ke gabashin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa yawancin wadanda aka hallaka a kusa da birnin Deir al-Zour mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi.

Kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da Syria wato IS, ta bullo da sabbin hanyoyin kai hare-hare a gundumomin da gwamnatin Syria ke iko da su da kuma birane.

Wasu rahotannin sun ce an hallaka dakarun gwamnati da fararen hula a wasu biranen kasar.

A bangare guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai fargabar mutane 200,000 na fuskantar barazanar karancin abinci a Syria.